Messi ya ci kwallaye 500 a Barcelona

Asalin hoton, Getty Images
Messi ya fara ci wa Barcelona kwallo a cikin watan Mayun 2005, lokacin yana da shekara 17
Lionel Messi ya ci kwallo ta 500 a Barcelona a ranar Lahadi a wasan da suka doke Sevilla 2-1 a ranar Lahadi a gasar La Liga wasan mako na 11 da suka yi.
Messi mai shekara 29, ya ci wa Barca kwallaye 500 a wasanni 592 da ya buga mata tamaula, ciki har da wasannin sada zumunta.
Dan wasan ya fara ci wa Barcelona kwallo a cikin watan Mayun 2005, a lokacin yana da shekara 17.
Yanzu haka dan kwallon na Argentina ya bai wa Paulino Alcantara tazarar kwallaye 105, wanda ya rike matsayin dan wasan da ya fi ci wa kungiyar kwallaye a shekarar 1912 da 1927.
A cikin watan Afirilu ya ci kwallo na 500 a wasannin da ya buga wa kasarsa da Barcelona a karawar da suka ci Valencia 2-1.
Messi ya zura kwallaye 320 a manyan wasannin Spaniya da kuma 90 da ya ci a gasar cin kofin zakarun Turai, sauran ya ci su ne a Uefa Super Cup da gasar kofin duniya ta zakarun nahiyoyi.