Ibrahimovic ya ci kwallo na 25,000 a tarihin Premier

Asalin hoton, Getty Images
Yadda Ibrahimovic ya yi murnar kwallon da ya ci ta 25,000 a gasar Premier
Zlatan Ibrahimovic ya ci kwallo na 25,000 a tarihin gasar Premier a ranar Lahadi, a wasan da Manchester United ta doke Swansea City 3-1.
Paul Pogba ne ya fara ci wa United kwallo kuma na 24,999, yayin da Ibrahimovic ya kara ta biyu a minti na 21 kuma ta 25,000 da aka ci a gasar ta Premier.
Haka kuma ta uku da Ibrahimovic ya ci wa United ita ce ta 400 da ya zura a raga tun lokacin da ya fara murza-leda a matsayin kwararren dan kwallo.
Wannan ne karon farko da United ta ci kwallon kirgen tarihi a gasar Premier, sai dai kuma ita ce aka fara ci a gasar Premier da aka fara a shekarar 1992.
Kuma Brian Deane ne ya zura wa United kwallo da ka a raga, a lokacin da suka fafata da Sheffield United a shekarar.