Ronaldo zai kara shekara 10 a Real bayan 2021

La Liga

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto,

Ronaldo na son yin ritaya idan ya kai shekara 41 da haihuwa

Cristiano Ronaldo ya ce zai iya ci gaba da taka leda a kungiyar zuwa shekara 10, idan yarjejeniyar da ya sake kullawa da kungiyar ta kare.

Kwantiragin Ronaldo mai shekara 31, da Real Madrid na shirin karewa a watan Yunin 2018, amma ya tsawaita ta, inda zai kai karshen kakar wasan 2021.

Dan kwallon na tawagar Portugal ya ce ba wannan ba ne karo na karshe da zai tsawaita yarjejeniyar ci gaba da wasa a Madrid, yana fatan sai ya kai shekara 41 kafin ya yi ritaya.

Ronaldo ya ci kwallaye 371 tun lokacin da ya koma Madrid da taka-leda daga Manchester United a shekarar 2009.