Ana zargin Neymar da Barcelona da zamba

Barcelona

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

A shekarar 2013 Neymar ya koma Barcelona daga Santos

Wani alkali a Spaniya ya ce ya kamata a gabatar da Barcelona da Neymar gaban kotu, kan zargin zamba, wata guda bayan da aka janye karar da aka shigar tun farko.

A ranar Litinin wata gidauniya mai suna DIS ce ta bukaci a sake sauraren karar, inda ta ce an yi mata cogen a lokacin da Neymar ya koma Barcelona daga Santos a shekarar 2013.

Gidauniyar ce ke kula da hakkin dan kwallon na Brazil a harkar sauya kungiya.

Zargin da Neymar da iyayensa suka karyata, wanda daga bisani aka kuma kori karar tun a cikin watan Yuni.

A cikin watan Satumba, babbar kotun Spaniya karkashin Alkali Jose de la Mata ya bayar da umarnin da a sake sauraren karar.

Dan wasan ya tsawaita zamansa a Barcelona kan yarjejeniyar shekara biyar a cikin watan Oktoba.

Tun a baya an umarci Barcelona ta biya tarar kudi fam miliyan 4.7, saboda kokarin kauce wa biyan haraji kan cinikin Neymar.

An bai wa masu shigar da kara na Spaniya kwanaki 10 da su shirya gabatar da Barcelona da Neymar gaban kuliya.