Barca ta kalubalanci katin da aka bai wa Messi

La Liga

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

An bai wa Lionel Messi katin gargadi a minti na 83, a lokacin Barcelona ta ci Sevilla 2-1

Kungiyar Barcelona ta daukaka kara game da katin gargadi da aka bai wa Lionel Messi saboda ya bata lokaci yayin wasan da suka ci Sevilla 2-1 a gasar La Liga ranar Lahadi.

An bai wa Messi katin gargadin ne bayan da ya yi kokarin mayar da takalminsa da ya fice daga kafarsa sakamakon karo da ya yi da dan kwallon Sevilla Steven N'Zonzi, bayan dawowa daga hutu.

Kociyan Barcelona, Luis Enrique, ya ce igiyar daure takalmin dan wasan ce ta tsinke.

A wasan ne Messi ya ci wa Barcelona kwallo na 500 a tarihi, tun lokacin da ya koma can da murza leda.