Toni Kroos zai yi jinya

La Liga

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kross ya tsawaita yarjejeniyar ci gaba da taka leda a Real Madrid

Likitocin Real Madrid sun tabbatar da cewar dan kwallon tawagar Jamus, Toni Kross, ya yi rauni.

Dan kwallon ya yi rauni ne a karawar da Madrid ta ci Leganes 3-0 a ranar Lahadi a gasar La Liga da suka fafata.

A makon jiya ne, Toni Kross, ya sabunta yarjejeniyarsa da Real Madrid domin ci gaba da buga mata tamaula zuwa 2022.

Dan kwallon mai shekara 26, wanda ya koma Bernabeu daga Bayern Munich a shekara 2014, ya ci wa Madrid kwallaye hudu a wasanni 108 da ya buga mata