Fatma Samoura za ta kai ziyara Saliyo

Fifa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Fifa za ta iya dakatar da Saliyo idan ta fahimci cewar gwamnati na tsoma baki a harkar tamaular kasar

Sakatariyar Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya, Fifa, Fatma Samoura, za ta ziyarci Saliyo domin sasanta rikici tsakanin hukumar kwallon kafar kasar da shuwagabannin siyasar kasar.

Fifa ta bukaci yin taro tsakaninta da Shugaban kasar Saliyo, Ernest Bai Koroma, da kuma jami'an hukumar kwallon kafar kasar.

Haka kuma Samoura na son tattaunawa kan batun cogen wasa da ya shafi Saliyo a shekarar 2008.

A shekarar 2014 aka dakatar da 'yan wasa 15 da wasu jami'an Saliyo kan zargin cogen wasan da suka yi da Afirka ta Kudu a wasan shiga gasar cin kofin duniya.

Tun a farkon ba ne hukumar kwallon kafa ta Saliyo ta kafa kwamitin bincike ta kuma mikawa shuwagabannin kasar abin da ta gano, amma har yanzu ba a dauki mataki ba.