Inter ta dauki Pioli a matsayin kociyanta

Inter Milan

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Stefano Pioli ya horar da Lazio da Parma da kuma Bologna

Inter Milan ta nada tsohon kociyan Lazio, Stefano Pioli, a matsayin wanda zai horar da kungiyar.

Pioli mai shekara 51, ya saka hannu kan yarjejeniyar da zai ja ragamar kungiyar har zuwa Yunin 2018, zai kuma maye gurbin Frank de Boer wanda aka sallama, bayan kwanaki 85 da ya yi aiki.

Sabon kociyan zai fara jan ragamar kungiyar a wasan hamayya da za ta yi da AC Milan a San Siro a ranar 20 ga watan Nuwamba.

Shi ne kuma mai horar wa na tara da zai horar da kungiyar tun lokacin da Jose Mourinho ya bar Inter, bayan da ya lashe kofin zakarun Turai a shekarar 2010.