Gwarzon kwallon Afrika na BBC a 2016

Wanene zai lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na Afrika na BBC a bana
Bayanan hoto,

Wanene zai lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na Afrika na BBC a bana

A ranar Asabar ne za a bayyana biyar daga cikin 'yan takarar Zakaran Kwallon Afirka na BBC na 2016, kuma a soma kada kuri'a.

Za a sanar da sunayensu a wani shiri na musamman kuma kai tsaye a tashoshin BBC World TV (talabijin) da BBC World Service (rediyo), wanda za a fara da misalin karfe 6:00 na yamma agogon GMT.

Masoya kwallon kafar Afirka a duniya za su iya kada kuri'unsu a wannan daga karfe 6:50 na yamma agogon GMT.

Za kuma a rufe zabe ranar Litinin 28 ga watan Nuwamba da karfe 6:00 na yamma agogon GMT, sannan a bayyana wanda ya yi nasara a shirye-shiryen BBC Focus on Africa na rediyo da talabijin ranar Litinin 12 ga watan Disamba, da misalin karfe 5:35 na yamma agogon GMT.

Wadansu tsofaffin kwararrun 'yan kwallon kafar Afirka da masana kwallon kafa zasu halarci shiri na musamman ranar Asabar din.

Peter Okwoche ne zai gabatar da shirin, wanda zai hada da hira da wanda daya daga cikin wadanda suka lashe gasar a baya, da tattaunawa a kan 'yan takarar bana da kuma waiwaye a kan harkar wasannin kwallon kafa a Afirka a bana.

Za kuma ku samu damar kallon abubuwan da suka gudana a bayan fage a shafukan intanet na Facebook na BBC Africa da BBC Sport da kuma shafin Instagram.

Ku biyo mu a shafin intanet na BBC Hausa ma domin samun bayanai kai-tsaye a yayin kaddamar da shirin.

Shafin BBC Sport mai zai rika aikewa da sakwannin Twitter kai-tsaye a BBC Africa da BBC Sport.

Masu bibiyar mu a kafofin sadarwa na zamani ma za su iya kasancewa da shirin ta hanyar maudu'i #BBCAFOTY.