Sanchez ya yi rauni a wajen atisaye

Asalin hoton, AFP
Sanchez ya buga wa tawagar kwallon kafa ta Chile wasanni sama da 100
Dan kwallon Arsenal, Alexis Sanchez, ya yi rauni a lokacin da yake yin atisaye a tawagar kwallon kafa ta Chile.
Sanchez mai shekara 27, ba zai buga wa Chile wasan shiga gasar cin kofin duniya da za ta yi da Colombia a ranar Alhamis ba.
Sai dai likitocin tawagar Chile sun ce, dan kwallon zai iya murmurewa ya kuma buga wa kasar karawar da za ta karbi bakuncin Uruguay a ranar Talata.
Sanchez wanda ya ci wa Arsenal kwallaye takwas a kakar wasannin bana, ya buga wa kungiyar wasan da ta yi kunnen doki 1-1 da Tottenham a ranar Lahadi a gasar Premier.
Arsenal wadda ke mataki na hudu a kan teburin Premier, za ta ziyarci Manchester United a ranar 19 ga watan Nuwamba a gasar Premier wasannin mako na 12.