Brazil za ta karbi bakuncin Argentina

WC Qualifier

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Brazil na yin atisayen karbar bakuncin wasan hamayya da za ta yi da Argentina

Tawagar kwallon kafa ta Argentina za ta ziyarci Brazil domin buga wasan shiga gasar cin kofin duniya a ranar Alhamis.

A wasan farko da kasashen biyu suka fafata a gidan Argentina kunnen doki 1-1 da suka tashi.

Brazil wadda ke mataki na uku a jerin kasashen da suke kan gaba a taka-leda a duniya ta hadu da Argentina wadda ke matsayi na daya a jadawalin Fifa, sau 102.

Brazil ta ci wasanni 39, ita kuwa Argentina ta samu nasara a karawa 37, sannan suka yi canjaras a fafatawa 26.

Bayan da Kudancin Amurka suka yi wasanni 10, Brazil ce a matsayi na daya sai Uruguay sannan Equador, Argentina tana mataki na shida.

Ga sauran wasannin da aka za a yi:

  • Colombia vs Chile
  • Uruguay vs Ecuador
  • Paraguay vs Peru
  • Venezuela vs Bolivia