Kwarewar Lukaku ya wuce zama a Everton — Koeman

EPL
Bayanan hoto,

Kwantiragin Lukaku da Everton za ta kare a karshen kakar 2019

Kociyan Everton, Ronald Koeman, ya ce kwarewar da Romelu Lukaku yake da ita a fagen murza-leda ya fi karfin ya ci gaba da zama a kungiyar.

Koeman ya ce "Ina jin Lukaku ya hada komai a wasan kwallon kafa, ya kware wajen murza leda ya kuma iya cin kwallo yana da tsawo yana kuma da karfi".

Kwantiragin Lukaku da Everton za ta kare a karshen kakar 2019, ya kuma koma kungiyar da taka-leda ne daga Chelsea, inda yanzu haka ya ci mata kwallaye 68 a wasanni 137.

Koeman ya kwatanta salon kwallon da Lukaku ke buga wa da irin wadda tsohon dan kwallon tawagar Netherlands, Patrick Kluivert ya yi.