Takarar Gwarzon Kwallon Afirka: Dangarama Yaya Toure

Sau biyu Yaya Toure yana zama Gwarzon Kwallon Kafar Afirka na BBC, kuma sau hudu yana lashe kyautar Gwarzon Kwallon Kafar Afirka na Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka (CAF) - don haka ganin sunansa a jerin wadanda aka ware bana ba abin mamaki ba ne.

Ko da yake sau 23 kacal ya buga wasa a 2016, saka sunansa a cikin jerin ya nuna irin matsayinsa a fagen kwallon kafa a Afirka.

Kuma duk da cewa wasannin da ya buga ba su da yawa, tasirinsa ba ya misaltuwa.

A watan Fabrairu ya daga wa Manchester City Kofin Gasar League ta Ingila - inda ya fasa raga da wani bugun fanariti mai muhimmanci wanda ya ba su damar cin Liverpool a wasan karshe.

Ya kuma taimaka wa kungiyarsa kai wa matakin hudun karshe a Gasar Cin Kofin Zakarun Turai, ta kuma kare kakar wasannin bara a matsayi na hudu a teburin Gasar Premier, lamarin da ya ba su damar sake shiga gasar Turai.

Da wannan nasara Toure ya yanke shawarar ci gaba da zama a City duk da zuwan sabon koci Pep Guardiola, wanda a karkashin kulawarsa dan wasan ya bar Barcelona.

Amma bayan da ejan din Toure, Dimitri Seluk, ya yi ikirari cewa an ci mutuncinsa da ba a sanya shi a tawagar City da za ta buga wasannin Zakarun Turai na bana ba - abin da ya bata wa Guardiola rai - sai aka tura shi benci.

Asalin hoton, Alex Livesey

Bayanan hoto,

Yaya Toure na fatan lashe kyautar Gwarzon Kwallon Kafar Afirka na BBC a karo na uku

Kocin ya sha alwashin cewa Toure ba zai sake buga wasa a kulob din ba har sai Seluk ya nemi gafara. Ko da yake hakan ba ta faru ba, Toure da kansa ya ce a yi hakuri.

Ko da yake ba a son ranshi aka cire shi daga sahun farko na 'yan wasan kulob din nasa ba, shawarar Toure ta daina buga wa kasarsa wasa da kanshi ya yanke ta a shekarar 2016.

Kusan wata 18 ya dauka kafin ya yanke wannan shawara bayan nasarar da suka yi a Gasar Cin Kofin Nahiyar Afirka a Equatorial Guinea a 2015; duk da matsin lambar da ya sha a kan ya ci gaba da buga wa tawagar Elephants wasa.

Tsohon kocin tawagar Ivory Coast Francois Zahoui na cikin mutanen da suka yi yunkurin rarrashinsa ya ci gaba, kasancewar ana kan fafatawa don neman gurbi a Gasar Cin Kofin Afirka ta 2017 a Gabon da Gasar Cin Kofin Duniya ta 2018 a Rasha.

Ba sai an yi dogon nazari ba za a iya fahimtar dalilin haka.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Yaya Toure ya taimaka wa Ivory Coast ta lashe gasar cin kofin Afirka a 2015

Bayan ya kwashe shekara da shekaru yana fitowa da kuma muhimman kwallayen da ya ci, Toure ya taka muhimmiyar rawa ga Ivory Coast, sannan ya kammala yayinsa na yi wa kasar tasa wasa ta hanyar jagorantar su zuwa daukar Kofin Afirka a 2015.

Ya kuma taka leda a duk wasannin da Ivory Coast ta buga a zuwanta Gasar Cin Kofin Duniya har sau uku a jere.

Sai dai a shekarar 2016 ya yanke shawarar cewa lokaci ya yi da zai yi ritaya daga wasannin kasa-da-kasa - ko da yake ya ce yanke wannan shawara ba abu ne mai sauki ba.

Da yake rubuta sanarwar yin ritayar a watan Satumba, Toure ya ce, "Mai yiwuwa rubuta wannan sanarwa ne gasa mafi wahalarwa a rayuwata".

Amma ya yi bayani karara cewa ba ya tunanin tauraruwarsa a fagen wasan kwallon kafa na dusashewa.

"Kasancewar shekarata 33 a yanzu, da tsanantar atisaye, da yawan buga wasanni ba su ne suka sa na yanke wannan shawara ba", inji shi.