Takarar Gwarzon Kwallon Afirka: Gwanin gudu Sadio Mane
Kakar wasanni ta bana ta yi kyau sosai ga dan wasan tawagar Senegal, Sadio Mane.
Hazikin dan wasan na gaba zai iya taka leda a ko wanne bangare na filin wasa - a gefe, ko a baya, ko a gaba - sannan an wayi gari ya shiga sahun 'yan wasan Gasar Premier da suka fi barazana ga ragar abokan hamayya, kuma daya daga cikin 'yan wasan Afirka da suka fi kwazo.
Gudun dan wasan, da iya rike kwallo, da saurin tunani, su kan jefa tsoro a zukatan abokan hamayyarsa sun kuma dasa kaunarsa a zukatan 'yan kallo sun kuma jawo masa yabo daga masharhanta.
Yana da dabaru ba iyaka ga shi kuma kaifi daya a bakin raga, inda yake iya karbar kwallo ya kuma samar da dama ga abokan wasanshi.
Mady Toure, wanda ya kafa cibiyar koyar da kwallon kafa ta Academie Generation Foot inda Mane ya fara daukar darasin kwallo, ya yi amanna cewa dan wasan komai-da-ruwanka ne.
Ya shaida wa BBC cewa, "Sadio Mane na da wani abu wanda ko Lionel Messi bai da shi, wani abu da Neymar ma bai da shi".
Mane ya karkare kakar wasanni ta bara a matsayin dan wasan da ya fi ci wa Southampton kwallo, kasancewar ya ci kwallo 15 a gasa daban-daban sannan ya rattaba hannu a kan yarjejeniyar komawa Liverpool a kan kudi fam miliyan 34.
Asalin hoton, Matthew Ashton - AMA
Sadio ya samu shiga cikin 'yan kwallon Afirka da ake damawa da su a kakar wasannin da ta gabata
Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus
Kashi-kashi
End of Podcast
Da wannan komawa tasa Anfield, ya zamo dan wasan Afirka da ya fi kowa tsada a tarihi, saboda kudin da aka saye shi ya haura fam miliyan 28 din da Manchester City ta bai wa Swansea don sayen dan wasan gaba na Ivory Coast Wilfried Bony a watan Janairun 2015.
Mane ya ci kwallo shida, ya kuma taimaka an ci hudu a wasanni goman da ya buga a kakar bana.
Tun tashin farko ya fara taka rawar-gani a Liverpool, inda ya ci kwallonsa na farko ta gasa a kakar bana a wasan da suka ci Arsenal 4-3 a ranar farko ta gasar.
Haka kuma Mane ya yi tasiri sosai a wasa na gaba, lokacin da ya taimaka har sau biyu Liverpool ta lallasa Burton Albion da ci biyar da nema a Gasar Cin Kofin EFL.
Bayan nan kuma ya ci kwallo daya, ya kuma taimaka aka ci daya a wasan da suka yi a gida, inda suka yi nasara a kan masu rike da kambun Gasar Premier Leicester City, lamarin da ya kidima magoya bayansu.
Daya kwallon da ya ci kuma a nasarar da suka yi ne a kan Hull da West Brom da kuma kwallo biyu lokacin da suka lallasa Watford da ci 6-1.
A wasannin kasa-da-kasa kuma, Mane ya buga wa Senegal a wasansu na farko na neman gurbi a Gasar Cin Kofin Duniya ta 2018 a watan Oktoba, inda ya kara tabbatar da muhimmancinsa ya kuma ci kwallo mai muhimmanci wadda ta taimaka suka yi nasara a kan abokan hamayyarsu na Rukunin D, Cape Verde.
Asalin hoton, Getty Images
Sadio Mane na taka rawar gani sosai a Senegal da Liverpool
Mane ya buga wa kasarshi wasa sau 36, ya ci kwallo 10, ya kuma taimaka an ci wa tawagar ta Teranga Lions kwallo 11; zai kuma taka muhimmiyar rawa a fatan da suke da shi na isa Rasha a 2018 da ma Gasar Cin Kofin Kasashen Afirka a Gabon badi.
Rawar da Mane ya taka a kulob da ma wa kasarsa ita ta sa ya cancanci shiga cikin wadanda za a zabi Gwarzon Dan Kwallon Afirka na BBC na Bana daga cikinsu a karo na biyu a jere.
Tuni dai kwalliya ta fara biyan kudin sabulu dangane da shawararsa ta daina makaranta ya koma kwallon kafa yana da shekara 15 a duniya.
Ya lashe gasar league da kofin kalubale tare da kungiyar kwallon kafa ta FC Salzburg ta Austria a 2014, ya zama kirjin biki a tawagar Senegal, sannan kuma a watan Mayun 2015 ya kafa tarihi a matsayin wanda ya fi kowa saurin cin kwallo uku a tarihin Gasar Premier lokacin da ya fasa ragar Aston Villa har sau uku a cikin sakan 175 a madadin Southampton.
Daga lokacin da ya fara kwallon kan titi a garinsu, Sedhiou, zuwa tafiyarsa Gasar Premier ta hanyar Dakar, da Faransa, da Austria, Mane yana kayatarwa sosai.
Karewa da karau kuma ana ganin akwai yiwuwar ya zama daya daga cikin 'yan wasan da suka fi gwaninta a tarihin nahiyar Afirka.