Takarar Gwarzon Kwallon Afirka: Sarkin Yanka Riyad Mahrez

"Za ka iya tunanin cewa maganadisu ne a kafarsa idan yana murza leda."

Wadannan su ne kalaman da Madjid, abokin dan wasan da ke takarar zama Zakaran Kwallon Kafar Afirka na BBC na 2016, Riyad Mahrez, ya yi wajen bayyana irin gogewar dan wasan.

Madjid, wanda abokin Mahrez ne tun suna kanana, ya kara da cewa "A da mukan yi fada da juna domin kawai mu tabbatar Riyad ya buga wa bangarenmu wasa."

Ya tuna lokacin da suke buga kwallo tare suna yara a garin Beni Snous da ke arewa maso yammacin Algeria.

Yanzu dai dukkan duniya ta san irin bajintar da Mahrez yake nunawa a fagen kwallon kafa - da kuma yadda manya da kananan kungiyoyin kwallon kafa ke ruguguwar sa.

An yi ta rade-radin cewa Mahrez zai koma Arsenal ko Chelsea ko kuma Barcelona, bayan ya taka muhimmiyar rawa a mamakin da Leicester City ta bayar da ta lashe Gasar Premier ta 2016.

A kwanan baya ne kungiyar kwararrun 'yan wasa ta zabi dan kasar ta Algeria a matsayin dan wasanta na shekara - inda ya zama dan Afirka na farko da ya kai kan wannan matsayi - bayan ya taka muhimmiyar rawa inda ya ci kwallo 17 sannan ya taimaka aka zura kwallo 11 a wasannin league 34 da ya buga.

Asalin hoton, Catherine Ivill - AMA

Bayanan hoto,

Riyad Mahrez ya taka rawa a nasarar ban-mamaki da Leicester City ta lashe Gasar Premier

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

A kakar wasan da ta wuce ne Mahrez, wanda ya koma Leicester daga Le Havre, a kan kudi 'yan kadan, wato £400,000 a shekarar 2014, ya soma tashe kuma da shi da Leicester sun ci gajiyar wannan tashen.

Watakila daya daga cikin lokutan da ba za a manta da su ba shi ne ranar 6 ga watan Fabrairu a gidan zakarun kwallon kafa na wancan lokacin Manchester City, lokacin da Mahrez ya caki kwallo ya zagaye Nicolas Otamendi, ya shiga kafar Martin Demichelis wanda ya dankara kwallon a raga, inda Leicester ke gaban City da ci 2-0.

Leicester dai ta yi nasara a wasan da ci 3-1, kuma ganin cewa Mahrez ya bayar da gudunmawar kwallo uku a wasannin league bayan wancan wasan, hakan ya sa suka yi gagarumar nasara.

Shi ya sa ba a yi mamaki ba a wancan lokacin da kungiyoyin kwallon kafa suka yi ta son sayen sa.

Kungiyoyin sun rika yin gogayya domin sayen dan wasan, mai siririn jiki - domin kuwa Mahrez dan wasa ne da basirarsa da kazar-kazar dinsa da kuma iya murza ledarsa ke burge 'yan kallo da abokan wasansa.

Sai dai dan wasan, mai shekara 25, ya ki amincewa da zawarcin da kungiyoyin ke yi masa, ya yi zaman sa a Leicester domin ci gaba da bayar da tasa gudunmawar.

Babu ko tantama cewa Mahrez zakakurin `dan wasa ne, musamman idan aka yi la'akari da cewa ya girma ne a wajen garin Sarcelles na birnin Paris, kuma yana dan shekara 15 mahaifinsa Ahmed ya rasu sakamakon kamuwa da ciwon zuciya.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Riyad Mahrez da kasarsa Algeria suna taka rawar gani

Ya zuwa yanzu ya ci wa Leicester kwallo hudu a kakar wasa ta bana - uku daga cikinsu a Gasar Cin Kofin Zakarun Turai.

Kuma ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen ganin Algeria ta yi nasarar samun gurbi a Gasar Cin Kofin Afirka da za a yi a Gabon a shekara mai zuwa.

Abokin wasansa dan kasar Algeria, Mehdi Abied, ya bayyana shi da cewa "Riyad dan wasa ne da ke sanya kungiyar kwallon kafa ta yi suna. Kowa ya san Algeria ne saboda Riyad."

Ya kara da cewa "A kasar Algeria, muna alfahari da Riyad. Ba karamin aiki ba ne kasancewa zakaran Gasar Premier. Ba karamin al'amari ba ne.

"Kowanne mutum a Afirka yana kaunar Riyad. Zan iya tunawa lokacin da na je Habasha da tawagar kwallon kafar Algeria, inda 'yan kasar suka rika nuna goyon baya ga Riyad sama da tawagar kwallon kafar kasarsu!"