Takarar Gwarzon Kwallon Afirka: Dodon Raga Pierre Emerick-Aubameyang

Tun da ya soma buga kwallo a Borussia Dortmund, dan wasan gaba Pierre Emerick-Aubameyang na ci gaba da burge masoya kwallo.

Dan takarar na Zakaran Kwallon Kafar Afirka na BBC na 2016 na da shekaru 27, kuma ya taso ne a kasar Faransa. Yana cikin wadanda kungiyar kwallon kafar AC Milan ke nema, amma kuma har yanzu bai buga masu kwallo ba, bayan da ya je Dion na Faransa a matsayin aro.

A wani wasan sada zumunta wanda shi ne wasanshi na farko a shekarar 2008, lokacin yana da shekaru 18, ya burge manyan 'yan wasan da ke cikin tawagarsa.

Mai tsaron ragar Dion a wancan lokacin, Florent Perraud, ya ce, "Idan kana wasan sada zumuntarka na farko, duk ba a shirye ka ke ba, amma duk da cewa ba a shirye ya ke ba, ya fi duk sauran sauri da iya wasa."

Ya kara da cewa, "A lokacin da wasan ke gudana muna ta tambaya, 'wai waye wannan yaron ne, ko dai aljani ne aka kawo mana'.

"Mun gane cewa ba wai matashi ne kawai muka samu ba, mun samu wani gwarzo ne na musamman."

Bayan haka, Aubameyang ya zura kwallo 10 a kakar wasannin da ta biyo baya.

Asalin hoton, Lars Baron

Bayanan hoto,

Gudu, da yadda Pierre Emerick-Aubameyang ke murnar cin kwallo suna burge 'yan kallo

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Daga nan kuma rayuwar matashin wanda ya zauna a kasashen Faransa da Colombia da Italiya da Mexico (tunda yana yawo tare da mahaifinsa wanda shi ma dan kwallo ne), inda aka bayar da shi aro a kungiyoyin Lille da Monaco da St Etienne, daga nan kuma ya koma Faransa da zama na dindindin a shekarar 2011, a inda ya samu nutsuwar nuna basirarsa.

Daga nan ne kuma, a shekarar 2013 ya koma Dortmund, inda ya samu damar zama daya daga cikin gwarzayen 'yan wasan gaba a duniya.

A watan Yunin 2016, ya zamo dan kwallon Afirka na farko da ya lashe kyautar Gwarzon Dan Wasan Shekara na Bundesliga, inda manyan 'yan wasa suka kada kuri'ar zabensa.

Kwazonsa a kwallo kuma ya samar masa lakabin 'Auba', wanda shi ne dan kasar Gabon na farko da ya zamo Gwarzon dan wasan Afirka na CAF.

Ya yi fice ne musamman saboda irin kwallayen da ya ke sha - ya zura 11 a wasannin gasar Bundesliga tara a wannan kakar, ciki har da kwallo hudu da ya sha a nasarar 5-1 da suka yi a kan Hamburg - da kuma kwallo 89 cikin 152 jimla da ya sha wa Dortmund.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Pierre emerick-Aubameyang yana matukar haskakawa a gasar lig ta Jamus

Yana kuma da gudu, wanda har ya sa ake kwatanta shi da Usain Bolt - da kuma yadda ya ke nuna murnarsa bayan ya zura kwallo ta hanyar rufe fuskarsa da wasu alamu na Batman da Spiderman.

Abokin wasansa a Dijon Jordan Loties ya ce, "Yana barkwanci, da son sa mutane dariya, gaskiya yana da ban-dariya sosai kuma mutum ne na mutane."

Da tsalle-tsallensa da kuma kwalliyarsa da irin askin da ya ke yi, Aubameyang ya nuna irin yadda yake son burge jama'a - duk da cewa yana bayyana kansa a matsayin mai kunya.

Aubameyang ya shaida wa Sashen Wasanni na BBC cewa, "Na yi aiki tukuru domin inganta wasana".

Ya yi maitar buga kwallo tun yana karami, inda ya ke da kayayyakin wasa da ya kera na 'yan kwallo da filayen kwallo a dakin kwanan sa, tun kafin ya shiga tawagar kwallon kafar yara kanana a Faransa.

Aubameyang ya gaji mahaifinsa wanda ya zamo kyaftin din tawagar kasar Gabon.