Takarar Gwarzon Kwallon Afirka: Gwanin rike kwallo Andre Ayew

Dan kwallon tawagar Ghana, Andrew Ayew ya nuna cewa shi ba mutum ba ne wanda gwiwarsa za ta yi sanyi a duk lokacin da ya samu kansa a cikin mawuyacin hali.

A watan Janairu an tilasta wa Ayew, mai shekara 26, buga kwallo ba a wurin da ya saba taka leda ba, lokacin da sabon kociyan Swansea, Francisco Guidolin, ya karbi aiki bayan da aka sallami Garry Monk, Amma ya bai wa marada kunya.

Kwarewarsa da kwazon da yake nunawa da kwallayen da yake ci, sun nuna karara irin burin da yake son cimmawa, kuma sun taimaka wajen hana Swansea rikitowa daga Gasar Premier.

Ayew ya ci kwallo biyu daga cikinukun da suka doke Liverpool, wanda daga karshe aka tabbatar da cewar Swansea za ta ci gaba da zama a Gasar Premier bara.

Saboda haka ba a yi mamaki ba da ya lashe kyautar bakon dan kwallon da ya fi taka rawar-gani a Swansea bara.

Ya nuna kwazo matuka; a watan Agusta ne West Ham United ta sayi Ayew a kan kudi fam miliyan ashrin da dubu dari biyar a matsayin dan kwallon kafa mafi tsada da ta dauka a tarihi.

Ayew ya yi rashin sa'a, bayan da ya yi rauni a ranar farko da yake yi wa West Ham wasa sabuwar kungiyar da ya koma da taka-leda.

Asalin hoton, Michael Regan

Bayanan hoto,

Andre Ayew ya sha alwashin taka rawar-gani fiye da mahaifinsa, Abedi Pele

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Bayan da ya yi jinyar watanni biyu, ya sake dawowa murza-leda a watan Oktoba.

Kuma kaguwa da aka gani a wajen Ayew, kamar irin wadda aka gani a wajen tsohon dan kwallon tawagar Ghana, Yaw Preko a lokacin da suka fara wasa tare ce ke tabbatar da cewa dan kwallon na son nuna cewa ba a yi zaben tumun-dare da kungiyar ta sayo shi ba.

A tawagar kwallon kafa ta Ghana kuwa Ayew ya ci gaba da zama fitatcen dan wasa a 2016.

Yana cikin 'yan wasan da suka ci wa Ghana kwallo a karawar da ta ci Mauritius 2-0, shi ne dan kwallon da ya fi taka rawar-gani a wasan da ya bai wa Black Stars gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka da za a yi a Gabon a shekara mai zuwa.

Duk da fama da jinya da ya yi a shekarar 2016, da kuma wasa a kungiyar da ba ta tagazawa, Ayew bai kasa nuna kansa a wajen cin kwallo ba.

Haka kuma yana da juriyar daukar matsi a rayuwarsa, kasancewa dan gidan fitatcen dan kwallon Ghana, Abedi Pele Ayew, ne wanda ake cewa shi ne dan kwallon kafa da babu kamarsa a Afirka.

Mahaifin Andre ya buga wa Ghana wasa 73, ya ci mata kwallo 33, ya kuma taimakawa kasar ta lashe kofin nahiyar Afirka a 1982 ta kuma hau mataki na biyu a 1992.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Andre Ayew na fatansake lashe wannan gasa a karo na biyu

Ya kuma dauki Kofin Zakarun Turai a Marseille a shekarar 1993, suka kuma yi rashin nasara a wasan karshe shekara biyu bayan nan a Gasar Zakarun Turai.

Sai dai Ahmed Brynes, kociyan Nania ta Ghana, inda Ayew ya fara murza-leda da nufin gadon sana'ar da mahaifinsa ya yi, ya yi wani hasashe mai ban mamaki.

Brynes ya shaida wa BBC cewa, "Tun lokacin da Ayew ke shirin cika shekara 14, yake taka leda ta ban mamaki, kuma a lokacin ne yake cewa yana son ya taka rawar-gani fiye da mahaifinsa".

"Na fada masa cewa 'mahaifinka ya kafa tarihin da wuya a kamo shi...', amma sai ya ce min shi zai kafa sabon tarihi, kuma lokaci ne zai ba shi damar hakan".

A shekarar 1992 BBC ta bayyana Abedi Pele Ayew a matsayin Gwarzon Kwallon Kafar Afirka; dansa Andre Ayew ya bi sahun mahaifinsa inda ya lashe kyautar a shekarar 2011. Shin ko wannan ce shekarar da zai dara mahaifinsa a tarihi?