Ingila ta doke Scotland da ci 3-0

WCQ
Bayanan hoto,

Kwallon da Daniel Sturridge ya fara ci a ragar Scotland

Ingila ta samu nasarar doke Scotland da ci 3-0 a wasan shiga gasar cin kofin duniya da suka fafata a ranar Juma'a a Wembley.

Daniel Sturrige ne ya fara cin kwallo da ka tun kafin a je hutun rabin lokaci.

'Yan wasan Scotland Grant Hanley da kuma James Forrest sun barar da damar cin kwallo, daga nan ne Ingila ta kara zura biyu ta hannun Adam Lallana da Gary Cahill.

Wannan ne wasan da Ingila ta ci abokiyar hamayyarta Scotland kwallaye da yawa, wanda rabon da ta yi hakan tun a shekarar 1975.

Ingila ce ke matsayi na daya a kan rukuni na shida, ita kuwa Scotland tana mataki na biyar.