Ya kamata a bai wa Southgate horar da Ingila - Rooney

WCQ

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ingila tana mataki na daya a kan teburin rukuni na shida

Kyaftin din tawagar kwallon kafa ta Ingila, Wayne Rooney, ya ce ya kamata a bai wa Gareth Southgate aikin jan ragamar Ingila zuwa lokaci mai tsawo.

Southgate ya jagoranci Ingila lashe wasanni biyu daga guda uku da ya yi, inda a ranar Lahadi ya samu nasarar doke Scotland a wasan shiga gasar cin kofin duniya da ci 3-0.

Hakan ne ya sa Ingila ta dare mataki na daya a kan teburin rukuni na shida, bayan da ta yi wasanni hudu.

A kuma ranar Talata ne kociyan zai ja ragamar Ingila a wasan sada zumunta da za ta yi da Spaniya.

Southgate ya karbi aikin rikon kwarya na horar da tawagar Ingila, bayan da hukumar kwallon kafar kasar da Sam Allardyce suka raba gari.