Nigeria ta hada maki uku a kan Algeria a ranar Asabar

WCQ

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Nigeria tana mataki na daya a kan teburin rukuni na biyu

Tawagar kwallon kafa ta Nigeria ta doke ta Aljeria da ci 3-1 a wasan shiga gasar cin kofin duniya da suka fafata a filin wasa na Uyo da ke Akwa Ibom a ranar Asabar.

Nigeria ta fara cin kwallo ta hannun Victor Moses a minti na 26 da fara tamaula, sannan kyaftin din Super Eagles, John Mikel Obi, ya ci ta biyu daf da za a je hutu.

Bayan da aka dawo ne Algeria ta farke kwallo daya ta hannun Nabil Bentaleb, sai dai daf da za a tashi Victor Moses ya ci wa Nigeria kwallo na uku kuma na biyu da ya ci a fafatawar.

Daya wasan na rukuni na biyu tsakanin Kamaru da Zambiya tashi suka yi kunnen doki 1-1.

Da wannan sakamakon Nigeria ce ta daya a kan teburi da maki shida, sai Kamaru ta biyu da maki biyu, yayin da Zambia da Algeria ke da maki daya-daya.

Nigeria za ta karbi bakuncin Kamaru a ranar 27 ga watan Agustan 2017, inda a ranar ne Algeria za ta ziyarci Zambia.