Wasannin damben Dei-Dei an tashi canjaras

Dambe
Bayanan hoto,

Manyan wasanni hudu aka dambata a Dei-Dei da ke Abuja, Nigeria

Manyan wasannin damben gargajiya da aka yi a gidan damben Ali Zuma da ke Dei-Dei a Abuja, Nigeria a ranar Lahadi, an tashi babu karawar da aka yi kisa.

An fara ne da sa zare tsakanin Aminu Shagon Mahaukaci Teacher daga Arewa da Dan Sama'ila Shagon Alabo daga Kudu a turmi uku da suka taka babu wanda ya je kasa.

An kuma raba rana tsakanin Nuran Dogon Sani daga Arewa da Garkuwan Shagon Alabo daga Kudu har tumi uku babu kisa, alkalin wasa Tirabula ya raba su.

Shi ma wasan Dogon Minista daga Kudu da Bahagon Abban Na Bacirawa turmi ukun suka yi babu wanda ya je kasa.

Damben karshe da aka yi da safiyar Lahadi, tsakanin Autan Faya daga Kudu da Shagon Bahagon Musan Kaduna turmi biyu suka yi aka tashi daga fili babu wanda ya yi nasara.