Real Madrid ta yi wasa 28 ba a doke ta ba

La Liga

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Real Madrid tana mataki na daya a kan teburin La Liga

Real Madrid ta yi wasa 28 a jere ba tare da an doke ta ba a dukkan fafatawar da ta yi tun daga kakar bara zuwa bana.

Madrid - karkashin jagorancin Zinedine Zidane - ta fara da doke Eibar 4-0 a ranar 9 ga watan Afirilun 2016, daga nan ta ci wasa 9 jumulla daga 11 da ta yi, daga nan ta lashe kofin zakarun Turai na 11 a Milan.

Real Madrid ta fara da lashe UEFA Super Cup a kakar bana, kuma a kakar shekarar nan ta yi wasa 17 ta lashe guda 12 ta yi canjaras a fafatawa biyar, sannan tana mataki na daya a kan teburin La Liga.

Jumulla Madrid ta yi wata takwas ba ci ta a wasa ba a jere ta samu nasara a karawa 21 da kuma yi canjaras a wasa bakwai.

Hakan na nufin kungiyar ta yi gumurzu sau 18 a gasar La Ligar Spaniya, sannan ta yi guda takwas a gasar cin kofin Zakarun Turai, ta kuma buga sauran wasannin a Copa del Rey da UEFA Super Cup.