Za mu iya kai wa gasar kofin duniya — Bale

WCQ

Asalin hoton, Huw Evans picture agency

Bayanan hoto,

Gareth Bale ya ci wa Wales kwallo na 26 a karawar da suka yi da Serbia a ranar Asabar

Dan wasan tawagar kwallon kafa ta Wales, Gareth Bale, ya ce suna da kwarin gwiwar cewar za su samu tikitin shiga gasar cin kofin duniya duk da kunnan doki 1-1 da suka tashi da Serbia a ranar Asabar.

Kasashen biyu sun fafata ne a wasan shiga gasar cin kofin duniya, inda Bale ya fara ci wa Wales kwallo daga baya Aleksandar Mitrovic ya farke ta da ka.

Da wannan sakamakon Wales tana mataki na uku a kan teburin rukuni na hudu, inda Jamhuriyar Ireland wadda ke mataki ta ba ta tazarar maki hudu, za kuma su fafata a tsakaninsu a Dublin a ranar 24 ga watan Maris.

Wasan da Wales ta yi a ranar Asabar a filinta da ke Cardiff shi ne na uku da tawagar ta yi canjaras a fafatawa uku a jere, kuma ita ce ke fara cin kwallo daga baya a farke.