Masar ta doke Ghana da ci 2-0

WCQ

Asalin hoton, Mujahid Safodien/Getty Images

Bayanan hoto,

Mohammed Salah ya ci Ghana kwallo a bugun fenatiti

Tawagar kwallon kafa ta Ghana ta yi rashin nasara a hannun ta Masar da ci 2-0 a wasan shiga gasar cin kofin duniya da suka fafata a Askandariya a ranar Lahadi.

Mohamed Salah da Abdallah Saied ne suka ci wa Masar kwallayen biyu.

Hakan na nufin Masar tana mataki na daya a kan teburin rukuni na uku.

Ghana wadda ta hada maki daya a wasanni biyu da ta yi ta shiga tsaka mai wuya, sai dai kuma saura karawa hudu a kammala wasannin neman shiga gasar cin kofin duniyar.

Rabon da Masar ta halarci gasar cin kofin duniya tun a shekarar 1990.