Ingila za ta karbi bakuncin Spaniya

Friendly

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ingila ta ci Scotland 3-0 a wasan shiga gasar cin kofin duniya a Wembley

Tawagar kwallon kafa ta Spaniya za ta ziyarci ta Ingila a wasan sada zumunta da za su fafata a ranar Talata a Wembley.

Kasashen biyu sun kara a manyan wasanni har sau 24, Ingila ta samu nasara a karawa 12, Spaniya ta ci wasanni tara, suka yi canjaras a fafatawa uku.

Karawar karshe da kasashen suka yi a wasan sada zumunta, Spaniya ce ta samu nasara da ci 2-0 a kan Ingila a ranar 13 ga watan Nuwambar 2015.

A ranar Juma'a Ingila wadda ke mataki na 12 a jerin kasashen da suke kan gaba wajen murza-leda a duniya ta doke Scotland da ci 3-0 a wasan shiga gasar cin kofin duniya da suka yi a Wembley.

Ita kuwa Spaniya wadda ke matsayi na 10 a jadawalin Fifa da ta fitar na wadanda ke kan gaba a fagen tamaula a duniya, doke Macedonia 4-0 ta yi a ranar Asabar.