Griezmann ba zai buga karawa da Real ba

La Liga

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

A cikin watan Yuni Antoine Griezmann ya tsawaita yarjejeniya ci gaba da murza-leda a Atletico

Watakila dan wasan Atletico Madrid, Antoine Griezmann, ba zai buga karawar da kungiyar za ta yi da Real Madrid a ranar Asabar, sakamakon raunin da ya yi.

Griezmann ya yi rauni ne a fafatawar da Faransa ta ci Sweden 2-1 a wasan shiga gasar cin kofin duniya da suka yi a ranar Juma'a.

Tuni dan kwallon ya koma Spaniya domin yin magani, kuma hakan na nufin ba zai buga wasan sada zumunta da Faransa za ta yi da Ivory Coast ba a ranar Talata.

Atletico ce za ta karbi bakuncin Real Madrid a wasan hamayya a gasar cin kofin La Liga wasannin mako na 12 a ranar Asabar.

Griezmann mai shekara 25, shi ne dan wasan Atletico da ya fi yawan ci wa kungiyar kwallaye a kakar bana, inda ya ci guda shida.