Southgate na son sanin makomarsa a Ingila

England

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Southgate ya ci wasanni biyu da canjaras daya a karawa uku da ya horar da tawagar kwallon kafa ta Ingila

Kociyan rikon kwarya na tawagar kwallon kafa ta Ingila, Gareth Southgate, ya ce nan da wata daya yana son sanin idan hukumar kwallon kafar kasar za ta tabbatar ma sa aikin horar da tawagar.

A ranar Talata Southgate mai shekara 46, zai jagoranci Ingila a wasan sada zumunta da Spaniya a Wembley, kuma karawa ita ce ta karshe da aka yi yarjejeniyar zai horar da kasar.

Kociyan ya samu maki bakwai a guda tara da ya kamata ya samu a wasannin shiga gasar cin kofin duniya, kuma Ingila ce ke mataki na daya a kan teburin rukuni na shida.

Tuni hukumar kwallon kafa ta Ingila ta nada kwamitin da zai dauki sabon kociyan Ingila, inda ake ganin watakila a bai wa Southgate aikin jan ragamar tawagar na lokaci mai tsawo.

Southgate ya karbi aikin horar da Ingila na rikon kwarya bayan da hukumar kwallon kafar kasar da Sam Allardyce suka raba gari.