Lampard zai bar buga-leda a New York City

Asalin hoton, Getty Images
Shekara biyu Lampard ya yi a New York har da wasa aro
Tsohon dan kwallon Chelsea, Frank Lampard, ya ce zai bar taka-leda a kungiyar New York City wadda take buga gasar Amurka.
Lampard mai shekara 38, wanda yarjejenirsa za ta kare a kungiyar a karshen shekarar nan, ya rubuta a shafinsa na sada zumunt na Instagram cewa lokacin da zai bar kungiyar ya yi.
Dan wasan ya ce a nan gaba kadan zai sanar da sabuwar kungiyar da zai koma da taka-leda.
Lampard ya ci kwallaye 15 a wasanni 31 da ya buga wa New York a shekara biyu da ya yi, ya kuma buga wasanni aro a Manchester City.
Dan wasan ya bar Chelsea a shekarar 2014 a matsayin wanda ya fi ci wa kungiyar kwallaye a tarihi, inda ya ci guda 211.