An dage karawa tsakanin Madrid da Valencia

Fifa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Madrid za ta buga wasanta a gasar cin kofin duniya na zakarun nahiyoyi a ranar 15 ga watan Disamba

Hukumar kwallon kafa ta Spaniya ta dage wasan cin kofin La Liga tsakanin Real Madrid da Valencia wanda aka tsara za su kara a ranar 18 ga watan Disamba.

An dage karawar ne saboda da Madrid za ta buga wasan gasar cin kofin zakarun nahiyoyi da za a yi a cikin watan Disamba, inda za ta wakilci nahiyar Turai, bayan da ta ci kofin zakaru na 11 na Turai a tarihi.

Tun farko an tsara cewar Real Madrid za ta ziyarci Valencia a wasannin mako na 16 a gasar cin kofin La Liga a ranar Lahadi 18 ga watan Disamba, amma an dage wasan zuwa wani lokaci.

Madrid wadda ta lashe kofin duniya na zakarun nahiyoyi a shekarar 2014, tana mataki na daya a kan teburin La Liga da maki 27, yayin da Valencia ke matsayi na 15 da maki 10.