Nasri: Guardiola na hana 'yan wasa jima'i

Pep Guardiola

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Guardiola na hana 'yan wasansa jima'i da daddare domin su tashi da kuzari

Dan wasan kasar Faransa Samir Nasri ya bayyana daya daga cikin sirrin nasarar Pep Guardiola, inda ya ce, kociyan yana hana 'yan wasansa jima'i ne da dare.

Nasri ya sheda wa tashar talabijin ta Faransa, cewa kocin dan Spaniya yana ba wa 'yan wasa umarnin ka da su yi jima'i bayan karfe 12 na dare.

Dan wasan na Manchester City, wanda ya tafi Sevilla aro ya ce kocin yana sa wannan doka ne ko da kuwa babu wani wasa da kungiyarsa za ta yi washegari, domin 'yan wasan su samu barci sosai.

Hatta Lionel Messi ma, wanda ake dauka kusan gwarzon dan wasan duniya, kocin ba ya ware shi daga wannan doka, a lokacin yana Barcelona.

Nasri ya ce saboda haka ne ma Messin ba ya jin raunin da ya shafi jijiya ko tsoka