Marcelo ya cika shekara goma a Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid tana mataki na daya a kan teburin La Liga
Dan wasan tawagar kwallon kafa ta Brazil, Marcelo Vieira, ya cika shekara goma yana taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid.
Madrid ta gabatar da Marcelo a gaban 'yan jarida a ranar 15 ga watan Nuwambar 2006, a lokacin yana da shekara 18.
Dan wasan mai tsaron baya, ya buga wa Real Madrid wasanni 372, ya kuma ci mata kwallaye 26 tun komawarsa can da taka-leda.
Marcelo ya lashe kofuna 12 a Real Madrid ciki har da kofin zakarun Turai biyu da kofin duniya daya na zakarun nahiyoyi da UEFA Super Cup biyu da na La Liga uku da Copa del Rey biyu da kuma Spanish Super Cup biyu.
Dan kwallon shi ne ke matsayi na biyu a matakin dan wasan waje da ya buga wa kungiyar wasanni da yawa, bayan Roberto Carlos wanda ya yi wasanni 527.