Keane na Hull zai yi jinyar shekara daya

Asalin hoton, Rex Features
Will Keane ya je wasanni aro a Wigan da QPR da Sheffield Wednesday da kuma Preston a lokacin da yake Manchester United
Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Hull City, Will Keane, zai yi jinyar shekara daya, sakamakon raunin da ya yi a gwiwarsa.
Keane mai shekara 23, ya yi rauni ne a karawar da kungiyarsa ta ci Southampton a ranar 6 ga watan Nuwamba.
Dan kwallon ya koma Hull City da murza-leda daga Manchester United a ranar 30 ga watan Agusta, kuma tuni ya yi wasanni shida a kungiyar.
Keane ya taba yin doguwar jinya a shekarar 2012 a rauni iri daya da wanda ya yi a yanzu a lokacin da yake taka-leda a matasan tawagar kwallon kafa ta Ingila masu shekara 19.
Hull City tana mataki na 18 a kan teburin Premier.