Alin Kanin Bello ya buge Shagon Reza Bunza

Damben gargajiya
Bayanan hoto,

A turmin farko Ali Kanin Bello ya doke Shagon Reza a gidan damben Legas

Ali kanin Bello ya buge Shagon Reza Bunza a dambatawar da suka yi da yammacin Talata a gidan dambe na Aminu Goje da ke Alaba Rago da ke jihar Legas.

Ali Kanin Bello dan damben Arewa ya yi nasarar doke Shagon Reza Bunza dan wasan Guramada a turmin farko da suka zare.

Wasa na biyu tsakanin Shagon Ummaru Mugu Guramada da Autan Yahaya Kwantagora daga Arewa tashi suka yi babu wanda ya je kasa.

Shikuwa Shagon Cindo Guramnada buge Autan Sunusi dan Bunza daga Arewa ya yi a turmi na uku.

Wasa na karshe tsakanin Shagon Ummaru Guramada da Dan Hussaini daga Jamus turmi uku suka yi babu kisa.