Buffon ya buga wa Italiya wasanni 167

Italiya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Buffon ya fara buga wa tawagar kwallon kafa ta Italiya a 1997

Mai tsaron ragar Italiya, Gianluigi Buffon, ya buga wa tawagar kwallon kafar kasar wasanni 167.

Buffon ya yi wasa na 167 a karawar da Italiya da Jamus suka ta tashi babu ci a wasan sada zumunta da suka yi a ranar Talata.

Dan kwallon ya fara buga wa Italiya tamaula a ranar 29 ga watan Oktoba a shekarar 1997, yana da shekara 19 da watanni tara.

A lokacin ya canji Gianluca Pagliuca a karawar da Italiya ta yi da Rasha a wasan shiga gasar cin kofin duniya na 1998.

Buffon ya fara buga tamaula a karamar kungiyar Parma a shekarar 1991 zuwa 1995 daga nan ne ya koma babbar kungiyar har zuwa shekarar 2001.

Daga nan ne kuma ya koma Juventus da murza-leda a shekarar 2001 wadda a yanzu ya yi wa wasanni 469.

Cikin kofunan da ya lashe har da na duniya da Italiya ta dauka a shekarar 2006, kuma kasar ta yi ta biyu a gasar cin kofin nahiyar Turai ta shekarar 2012.