Gerrard ba zai koma Celtic ba — Rodgers

Asalin hoton, Getty Images
Brendan Rodgers da Steven Gerrard sun yi tare a Liverpool daga shekarar 2012 zuwa 2015
Kociyan Celtic, Brendan Rodgers, ya karyata rade-radin da ake yi cewar Steven Gerrard zai koma kungiyar da ke buga gasar Scotland.
Sai dai kuma Rodgers ya ce Gerrard yana da kwarewar da zai iya taka rawar gani idan har ya koma horar da tamaula.
Gerrard ya sanar da yin murabus daga kungiyar LA Galaxy ta amurka, dalilin da ya sa ake cewa zai koma Celtic yin aiki tare da kociyan da ya horar da shi a Liverpool.
Dan kwallon mai shekara 36, ya koma Galaxy a shekarar 2015, ya kuma ci kwallaye biyar a wasanni 34 da ya buga mata a kakar wasanni biyu.
Gerrard ya yi wa Liverpool wasanni 710 a tsakanin 1998 zuwa 2015.