Madrid za ta yi wasanni tara kafin kirsimeti

Spain

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Real Madrid tana mataki na daya a kan teburin La Liga

Real Madrid za ta yi wasanni tara kafin kirsimeti, a manyan wasanni dabam-dabam har guda hudu.

Fafatawar da za ta yi ta hada da gasar cin kofin La Liga da ta zakarun Turai da Copa Del Rey da kuma kofin duniya na zakarun nahiyoyi.

Madrid za ta fara buga wasan hamayya a gasar La Liga inda za ta ziyarci Atletico Madrid a ranar Asabar 19 ga watan Nuwamba.

Kwanaki uku tsakani Real za ta ziyarci Portugal domin fafatawa da Sporting Club a wasan cin kofin zakarun Turai, karawa ta biyar ta cikin rukuni.

Daga nan ne kuma kungiyar za ta buga wasanni uku a gasar La Liga da suka hada da gumurzu da Sporting da Barcelona da kuma Deportivo.

Sauran wasannin da Real Madrid din za ta yi kafin karshen shekarar nan sun hada da wasan cin kofin zakarun Turai da za ta yi da Borrussia Dortmund da Copa del Rey da Cultural Leonesa da kuma wasa daya a gasar cin kofin duniya na zakarun nahiyoyi.

Real Madrid tana mataki na daya a kan teburin La Liga da maki 27, bayan da ta yi wasanni 11 a bana.