Messi zai yi ritaya a Barcelona — Bartomeu

La Liga

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Lionel Messi ya ci wa Barcelona kwallaye 500

Shugaban Barcelona, Josep Maria Bartomeu, ya ce yana sa ran Lionel Messi ba wai zai tsawaita zamansa a kungiyar ba ne, zai ci gaba da wasa ne har sai ya yi ritaya a Camp Nou.

Bartomeu ya ce hankalinsa a kwance yake cewar za su sake kulla sabuwar yarjejeniya da dan kwallon Argentinan, kamar yadda suka yi da Neymar.

Sauran watanni 18 kwantiragin Messi ya kare a kungiyar Barcelona, wadda tuni ta tsawaita zaman Neymar a Camp Nou zuwa shekarar 2021.

Haka kuma shugaban ya ce suna tattaunawa da Luis Suarez domin shi ma ya amince da sabon kwantiragin da za su yi ma sa ta yi mai tsoka.