FA ta kara cin tarar Mourinho bisa kalamansa

Premier

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Manchester United za ta kara da Arsenal a gasar Premier a ranar Asabar

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta sake cin tarar Jose Mourinho, saboda kalaman da ya yi kan alkalin wasa Anthony Taylor, inda ta ce kalaman kocin sun nuna duk yadda lafirin ya yi ba zai tsira ba.

Taylor shi ne ya hura karawar da Liverpool da Manchester United suka tashi canjaras a gasar Premier da suka yi a Anfield a watan jiya.

Hukumar ta ce Mourinho ya biya tarar fam 50,000 kan kalaman da ya yi cewar zabo alkalin wasa Taylor ya saka matsi kan jami'an Manchester United.

A ranar Laraba hukumar ta ce kalaman nasa na nufin ta kowanne fanni alkalin wasan na tsaka mai wuya, ko ya taka rawar gani ko kuma bai yi ba.

Bayan tarar da hukumar ta ci Mourinho ta kuma gargade shi da ya guji sake jefa kansa cikin irin wannan lamari wanda ya yi.