Zakarun Turai: Kudin da Man United ke samu ya ragu

Manchester United

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Bashin United din ya karu zuwa fan miliyan 337.7, karin kashi 18 cikin dari

Kudin da Manchester United take samu ya ragu sakamakon kasa samun cancantar shiga gasar cin kofin Zakarun Turai ta Uefa, ta bana da ta yi.

Kudin da kungiyar take samu a cikin watanni uku na farkon shekara zuwa 30 ga watan Satumba ya ragu da fam miliyan 3.4, (kashi 2.8 cikin 100).

Haka kuma kudin da take samu a ranar da take yin wasa ya ragu da kashi 32.3 cikin 100, inda kenan take samun fam miliyan 16.8. Ribar da take samu ta zama fam miliyan 6.2.

Abin da ya fi haddasa raguwar kudin da kungiyar ke samun shi ne, kasancewar wasannin da take yi a gida sun ragu da guda uku, idan aka kwatanta da wasannin da ta yi a daidai wannan lokaci a 2015.

Bashin da ake bin ta kuma ya karu ne da kashi 18 cikin dari zuwa fam miliyan 337.7, sakamakon faduwar darajar kudin Ingila, fam a kan dala tun lokacin da aka kada kuri'ar ficewar Burtaniya daga kungiyar Tarayyar Turai.

Babban darektan kungiyar ta Man United Ed Woodward, ya ce, '' Yanayin kudin da muke ciki a wannan lokaci ya nuna tasirin rashin shigarmu gasar cin kofin Zakarun Turai ta Uefa.''

Sai dai kuma kudaden da kungiyar take samu na tallace-tallace ya karu da kashi 4.4 cikin dari zuwa fan miliyan 74.3, inda ake sa ran kudin da take samu gaba daya a shekara ya kai tsakanin fam miliyan 530 da miliyan 540.

Kungiyar ta sayi 'yan wasa hudu a lokacin kasuwar sayen 'yan wasa da ta wuce, wadanda suka hada da dan wasan tsakiya na Faransa, Paul Pogba, wanda ya kasance mafi tsada a duniya kan fam miliyan 89 da kuma dan Sweden Zlatan Ibrahimovic.

Man United din yanzu ita ce ta uku a tebur din Premier, sannan ta kai wasan dab da na kusa da karshe na cin kofin kalubale na Lig (EFL Cup) na Ingila, amma kuma tana cikin hadarin kasa kaiwa zagayen sili daya kwale na gasar cin kofin Zakarun Turai na Europa, yayin da ya rage wasanni biyu.