An hukunta kungiyar Brazil saboda halayyar 'yar kocinsu

Asalin hoton, Getty Images
'Yar Renato Gaucho mai goyon bayan kungiyar Gremio ce ta dindindin
An hukunta Gremio ta Brazil bayan da 'yar kocin kungiyar Renato Gaucho, ta shiga fili yayin murnar da kungiyar ke yi saboda ta samu kaiwa wasan karshe na cin kofin kalubale.
Carolina Portaluppi, mai shekara 22 tana zaune ne a bencin 'yan wasan bayan fili da sauran jami'an kungiyar, amma ana tashi daga wasan sai ta bi sauran 'yan wasa cikin filin a lokacin murnar nasarar.
Babbar kotun laifukan harkokin wasa ta Brazil ta yanke hukuncin cewa kungiyar za ta yi wasanta na karshe na zagaye na biyu na gasar cin kofin, a wani garin maimakon gidanta.
Kotun ta ce ba wai ta yi hukuncin ba ne a kan kaunar da mahaifi ke yi wa 'yarsa ba ne, ta yi ne a kan yin abin da ya saba wa ka'ida.
Kotun ta kuma ci tarar kungiyar fam 6,995, sannan ta gargadi kocin da cewa mai yuwuwa za a yi masa wani hukuncin kuma nan gaba.
Kungiyar ta Gremio,wadda ta ce za ta daukaka kara kan hukuncin, ta doke Cruzeiro 2-0 a jumullar wasa biyu,gida da waje.
Nan gaba a wannan watan ne za ta yi wasan karshe gida da waje da kungiyar Atletico Mineiro.
Magoya bayan kungiyar da suka ji haushin abin da 'yar kocin ta yi, wanda ya jawo musu hukuncin, sun yi ta sukarta a shafukan intanet, wasu kuma na kare ta, amma ita ba ta ce komai ba.