Klopp: Coutinho na nan daram a Liverpool

Jurgen Klopp with Philippe Coutinho

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Klopp ya ce Coutinho ya yi yarinta ya bar Liverpool a yanzu

Kocin Liverpool ya ce Philippe Coutinho zai ci gaba da zama daram a Anfield sakamakon rade radin da ake yi cewa gwanin dan wasan zai bar kungiyar.

Dan wasan na Brazil mai shekara 22, ya taimaka wa kungiyar ta kai matsayin da take yanzu a teburin Premier, inda ya ci kwallo biyar, kuma ya bayar aka ci biyar.

Saboda tashen da yake yi a yanzu, shi ne ake rade radin cewa zai koma kungiyar Barcelona ko Real Madrid.

Jurgen Klopp ya ce, ''a ra'ayina ni dai dan wasan ya dace sosai da nan (Liverpool).''

Ya ce, ''dukkaninmu muna fata tare da ganin cewa damarsa na nan Liverpool. Abin da mutane ke mantawa da shi a kan Phil shi ne, har yanzu matashi ne.

A matsayinsa na dan shekara 24, yana da sauran aiki a gabansa, yana bukatar samun kwarewa sosai.''

Rabon da Liverpool ta fara gasar Premier da kyau kamar bana tun kakar 2008-09, inda yanzu take ta daya da maki 26 da kwallo 30 a wasa 11.

Kungiyar za ta yi wasanta na Premier na gaba a gidan Southampton, ranara Asabar.

Klopp bai damu da kudin da manyan kungiyoyin Turai ke zuba wa domin sayen 'yan wasa ba, da za su iya janye 'yan wasansa ba.

Ya ce, '' maganar ba ta kudi ba ce. Idan da kungiyar da za ta biya dan wasa linki biyun abin da muke biya, sai in sayar musu da dan wasa.''

Kocin dan Jamus ya kara da cewa, ''wanene ni da zan ce dan wasa kada ya yi tunanin iyalinsa, ko 'ya'yansa, ko jikokinsa, ko sauransu, amma dai ban ga wasu kungiyoyi da yawa a duniya da za su iya yin haka ba.''

Ya ce, ''muna samar da yanayi na yadda ba wanda zai so ya bar kungiyar, kuma a yanzu ba ni da wata fargaba, domin 'yan wasan na son zama a nan.''