Crystal Palace 1 Manchester City 2

EPL

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Yaya Toure ne ya ci kwallaye biyun da ya bai wa City damar samun maki uku a kan Crystal Palace

Crystal Palace ta yi rashin nasara a gida a hannun Manchester City da ci 2-1 a gasar Premier da suka fafata a ranar Asabar.

Manchester City ce ta fara cin kwallo ta hannun Yaya Toure saura minti shida a je hutun rabin lokaci.

Bayan da aka dawo daga hutu ne Crystal Palace ta farke ta hannun Connor Wickham.

Saura minti takwas a tashi daga wasan Yaya Toure ya kara cin ta biyu a raga, hakan ne ya kuma bai wa City damar samun maki uku a karawar.

Rabon da Toure ya yi wa City wasa tun watanni uku baya, kuma nasarar da kungiyar ta yi a kan Palace ya sa ta koma mataki na biyu a kan teburin Premier.

Palace wadda aka ci a karo na biyar a gasar bana ta koma matsayi na 16 a kan teburin Premier.