Ana son sai an ga baya na - Rooney

Asalin hoton, Getty Images
Wayne Rooney shi ne kyaftin din tawagar kwallon kafa ta Ingila
Dan wasan Manchester United, Wayne Rooney, ya ce hotunansa da ake ta wallafawa a kafar yada labarai a lokacin da yake tare da tawagar Ingila ana kokarin a zubar masa da kima ne.
Rooney kyaftin din Ingila ya nemi gafara kan hotunansa da aka dauka a yana yin da bai dace ba a lokacin wani bikin aure a otal din da aka sauke tawagar kwallon Ingila.
Dan wasan ya ce yadda aka dauki hotunan ya nuna karara yadda ake son a zubar masa da martabarsa.
Ya kara da cewar yana jin 'yan jarida na kokarin ganin bayansa a fagen kwallon kafa, wanda ba zai bari hakan ta faru ba.
Hukumar kwallon kafa ta Ingila za ta hana 'yan wasa fitar dare daga otal din da ta ajiye su a lokacin da suke tunkarar wasa.
Hukumar ta Ingila na binciken yadda 'yan wasanta bakwai suka fice a daren Asabar, kwanaki uku da za su yi wasan sada zumunta da suka tashi 2-2 da Spaniya.