Man United da Arsenal sun tashi 1-1

EPL

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

United da Arsenal sun tashi wasa 1-1

Manchester United da Arsenal sun tashi wasa kunnen doki 1-1 a gasar Premier wasan mako na 12 da suka fafata a ranar Asabar a Old Trafford.

United ce ta fara cin kwallo ta hannun Juan Mata bayan da aka dawo daga hutu.

Arsenal ta farke ta hannun Olivier Giroud daf da za a tashi daga fafatawar.

Da wannan sakamakon Arsenal ta hada maki 25, ita kuwa Manchester United tana da maki 19.

United za ta karbi bakuncin West Ham a wasan mako na 13 a ranar Lahadi, yayin da Arsenal za ta karbi bakuncin Bournemouth a Emirates.