Rooney ya ce an ci mutuncinsa saboda ya bugu da barasa

Wayne Rooney, England Captain

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Rooney ya ce, ''Abin kamar 'yan jarida na son kashe ni da raina ne.''

Wayne Rooney ya ce yadda aka yi ta yayata abin da ya yi a kwanan nan, kan shan barasa da ya yi ya bugu, bayan wasan Ingila da Scotland, an ci mutuncinsa, kuma ya lashi takobi cewa zai ba marada kunya, domin tashi ba ta kare ba.

Kyaftin din na Ingila, ya bayar da hakuri kan hotunansa da aka gani ya bugu da giya a wurin wani biki,a otal din da 'yan wasan Ingila suka sauka, lokacin wasan nasu da Scotland.

Rooney ya ce yadda aka yi ta yayata batun, ya nuna ba a daukarsa da mutunci.

Dan wasan Manchester United, ya ce lamarin ya nuna kamar 'yan jarida na son kashe shi ne tun bai mutu ba, kuma ya ce ba zai taba barin hakan ta faru ba.

Da yake magana bayan wasansu da Arsenal ranar Asabar, Rooney mai shekara 31, ya ce, ''ina kaunar yi wa kasata wasa, kuma ina alfahari da nasarorin da na yi kawo yau, amma kuma a sani har yanzu da saurana.''

Sakamakon halayyar ta Rooney, hukumar kwallon kafa ta Ingila, FA, ta haramta wa 'yan wasan kasar fitar dare a duk lokacin da suke karkashin ikonta domin yin wani wasa na kasa da kasa.

Har yanzu dai hukumar ta FA, tana bincike kan zargin cewa 'yan wasa da dama ne suka fita rakashewa har zuwa tsakar dare, a daren Asabar, kwanaki uku kafin su yi wasan sada zumunta 3-3 da Spain.