Chelsea ta karbe ragamar Premier

Diego Costa yana cin Middlesbrough

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Wannan ita ce kwallo ta goma da Costa ya ci a bana

Chelsea ta karbe jagorancin teburin Premier bayan da ta bi Middlesbrough har gida ta doke ta da ci 1-0, a wasan mako na 12 na gasar ta Premier.

Diego Costa ne ya ci wa Chelsea kwallon a minti na 41 da wasa, kuma dan wasan ya kasance jigo wajen kai hare-hare a wasan a bangaren Chelsea.

Wannan shi ne karo na farko da Middlesbrough ta yi rashin nasara a cikin wasanni hudu da ta yi.

Yanzu Chelsea ta tsallako da maki 28 ta wuce Liverpool wadda kafin wasan ita ce ta daya, da kuma Manchester City ta biyu, masu maki 27 kowacce, yayin da Boro take ta 15 da maki 11, mataki daya tsakaninta da faduwa daga tebur.