Ba za a hukunta Henderson da Lallana ba

Adam Lallana da JOrdan Henderson

Asalin hoton, others

Bayanan hoto,

Adam Lallana (hagu) da Jordan Henderson 'yan wasan Ingila ne da kuma Liverpool

Hukumar kwallon kafa ta Ingila FA ba za ta hukunta 'yan wasan kasar kuma na Liverpool ba Jordan Henderson da Adam Lallana, kan rahotannin cewa sun je wani gidan rawa na masu rawa tsirara a lokacin da suke cikin tawagar 'yan wasan kasar.

Ana zargin cewa 'yan wasan biyu sun je wannan gidan rawa ne bayan wasan da Ingila ta ci Scotland na neman zuwa gasar cin Kofin Duniya, kuma kasa da kwana uku kafin su yi canjaras a wasan sada zumunta da Spaniya.

Haka kuma an gano cewa hukumar ta FA ba ta nemi kyaftin din Ingilan Wayne Rooney ya nemi gafara ba, kan rahotannin cewa an ga hotunansa ya yi tatil da giya, bayan wasansu da Scotland, a wani taron bikin aure a otal din da 'yan wasan Ingilan suka zauna.

Rooney dai ya nemi gafara a wurin kocin Ingilan na wucin-gadi Gareth Southgate, kan wannan lamari.

Kuma dan wasan na Manchester United mai shekara 31, ya mayar da martani kan wannan ymadidi da aka yi masa da cewa, an yi ne domin a ci mutunncinsa.

Sannan ya ce, idan ana son kashe shi ne tun bai mutu ba, to da sauransa har yanzu, kuma zai ba wa marada kunya.