Mahrez: Ba na son tunanin faduwa daga Premier

Riyad Mahrez

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto,

Kwallo biyar Mahrez ya ci wa Leicester a bana

Dan wasan gefe na Leicester City Riyad Mahrez ya ce ba ya son yin tunanin faduwa daga Premier bayan da zakarun suka yi rashin nasara a karo na shida a bana.

A ranar Asabar ne Watford ta ci su 2-1, kuma a yanzu suna matsayi na 14 a tebur da maki 12 a wasa 12, maki biyu tsakaninsu da rukunin masu ficewa daga gasar.

Dan wasan ya ce, ''ba wata matsala. Muna bukatar mu ci gaba da aiki tukuru ne kamar yadda muka yi, kuma na tabbata za mu dawo cin wasanninmu,''

''Na san cewa muna da kyawun da za mu tsaya a Premier, ko ma fin hakan.''

Sabanin matsayinsu a gasar ta Premier, kungiyar na gab da samun kaiwa matakin 'yan 16 na cin kofin Zakarun Turai a shigarsu ta farko gasar.

Kawo yanzu sun yi nasara sau uku, da canjaras daya a wasanninsu hudu na rukuni, ba tare da an zura musu kwallo ko daya ba, kuma za su kara da Club Brugge ranar Talata.

Mahrez ya ce, ''bara bara ce, mu ne zakaru. Amma ko mu zakaru ne ko ba zakaru ba ne, wannan wata shekarar ce daban.

''Sauran kungiyoyi sun fi mu buri, kuma kowace kungiya burinta shi ne ta doke Leicester. Saboda haka dole ne mu kokarta, kuma na san za mu dawo ganiyarmu.''

Sunan Mahrez na cikini jerin 'yan wasa 23 da za a zabi gwarzon dan wasan hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa na 2016 a cikinsu, amma kuma ya kawar da yuwuwar samun matsayin.

Ya ce, ''akwai manyan 'yan wasan da suka fi ni. Ni dai farin cikina kawai shi ne da sunana a ciki,''