Arsenal: Bellerin ya sabunta kwantiragi

Hector Bellerin

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

A karawarsu Arsenal da Tottenham ne Bellerin ya ji rauni a agararsa

Dan wasan baya na Arsenal kuma dan Spain Hector Bellerin, mai shekara 21 ya sabunta kwantiraginsa na wani tsawon lokaci da kungiyar.

A watan Yuli na 2015 ne ya sabunta kwantiraginsa na tsawon wa'adi, amma kuma ake cewa zai bar Arsenal din ya koma tsohuwar kungiyarsa Barcelona ko Manchester City.

Bellerin ya ce,"na dade a nan, ina jin nan ya zama kamar gida a wurina, kuma wannan shi ne abin da ya fi dacewa na yi."

"ina matukar farin cikin cigaba da zama dan wasan Arsenal na karin wasu shekaru masu yawa a nan gaba."

Bellerin ya buga wa Arsenal manyan wasanni 67 da suka hada da 11 a bana kafin ya tafi jiyya ta tsawon makonni hudu.