Amurka ta kori kocinta Jurgen Klinsmann

Jurgen Klinsmann

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Klinsmann ya kai Jamus matsayi na uku a gasar kofin duniya ta 2006

Amurka ta kori kociyan tawagar kwallon kafarta tsohon dan wasan Jamus kuma kocin Jamus din na da Jurgen Klinsmann.

A shekara ta 2011 Klinsmann mai shekara 52, wanda ya dauki kofin duniya a matsayin dan wasa da Jamus a 1990, ya zama kocin Amurka.

Shugaban hukumar kwallon kafa ta Amurka Sunil Gulati ya ce, ''muna da kwarin guiwa muna da kwararrun 'yan wasan da za su taimaka mana samun zuwa gasar kocin duniya a Rasha a 2018"

''Amma yanayin yadda tawagar 'yan wasanmu da yadda cigabansu yake zuwa yanzu, ya sa muna ganin ya kamata mu sauya tsari.''

Klinsmann ya kai Amurka zagaye na biyu na gasar kofin duniya ta 2014 a Brazil bayan sun gama wasan rukuni a matsayin na daya a gaban Portugal.

Sai dai kuma Mexico ta ci su 2-1 kuma sun je gidan Costa Rica ta lallasa su 4-0 a wasanninsu na neman tikitin gasar cin kofin duniyar da za a yi na 2018.

Shugaban hukumar kwallon ta Amurka ya ce, '' a wasannin gaba da za a yi a karshen watan Maris, muna da isasshen lokacin da za mu sauya yanayin rukunin.''

Ya kara da cewa, '' muna bukatar hanyar da ta fi dacewa da za ta tabbatar da mun samu nasarar zuwa gasar kofin duniya ta takwas a jere.''

A da ana rade radin Klinsmann wanda tsohon dan wasan Tottenham ne shi ne zai zama kocin Ingila bayan barin Sam Allardyce a watan Satumba.